A wani munmunan rahoto da aka samu wata ranar Juma’a cikin farko-farkon shekarar 1921, kimanin shekaru 95 ke nan da suka wuce, wani jirgin ruwa mai suna “Conestoga” na dauke da sojojin ruwan kasar Amurka mutun 56, suka bace. Da misalin karfe 3:25pm na yamma, masu kula da tafiyar jirgi a ruwa suka bayyanar da bacewar jirgin, bayan ya taso daga tashar jiragen ruwa na sojojin ruwa a jihar Califonia, zuwa jihar Penssylvania.
Wata guguwa mai karfi ta nitsar da jirgin wanda hakan yasa duk mutanen da ke cikin jirgin suka rasa rayukan su. Amma cikin ‘yan shekarun nan sai wasu mutane suka tsinci wani jirgi a wani yanki na teku, bayan zurfafa bincike da masana suka gudanar a kan jirgin sun iya gano cewar lallai wannan jirgin shine jirgin da ya bace shekaru 95, da suka wuce.
Masanan sun bayyanar da cewar a waccan shekarar jirgin ya wuce layin da ya kamata yabi shi yasa ya nitse, a dai-dai lokacin da ake gudanar da taron juyayin mutuwar mutane 56, da dangin su, aka sanar da gano jirgin bayan tsawon shekaru. “yan uwa da abokan arziki sun garzaya wajen ganin jirgin don ganin inda 'yan uwan su, suka halaka.