Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Nau'u'u'kan Ciwon Ciki Da Kan Iya Hallakar Da Mutun


human stomach
human stomach

Kowane mutun nada ciki, wanda a kusan kowane lokaci mutun kan samu ciwon ciki da ke da nau’I daban-daban. Akwai wasu nau’in ciwon ciki da idan mutun yana jin su to lallai ya hanzarta ganin likita, domin kuwa wannan suna nuni da cewar akwai matsala da kan iya haifar da mutuwa.

A cewar masani Dr. Bandt, sun gudanar da wasu bincike akan jerin alamu na ciwon ciki da keda matukar hatsari ga rayuwar dan’adam. Sukace idan mutun yana yawan jin kunar zuciya, kamar zuciyar mutun daga tsakiya tana zafi, musamman idan mutun ya gama cin abinci, ta lallai wannan idan ya dauki lokaci mutun nasamun haka to ya garzaya asibiti.

Idan kuma cibiyar mutun na yawan ciwo, koda kuwa mutun yaci abinci ko kuwa, haka idan mutun yana samun kunar ciki idan yaci abinci mai zafi ko mai yaji to hakan kan iya zama wata cuta da shan wasu maguguna bazai magance ba, akwai bukatar mutun ya ga likita don ya duba yaga abun da ke damun mutun.

Hakama idan mutun kan samu ciwon gefen ciki akai-akai to shima yana da bukatar ganin likita, donmin kuwa ana iya dace da hanjin mutun sun sauka daga kan layin da yakamata, shi yasa mutun ke samun ciwon. Sai kuma wasu lokkuta mutane kan zauna da cutar nan da ke tara dattin ciki, idan kuma ba’a gaggauta aiki don cireta ba, to tana iya haifar da wasu matsaloli da dama a cikin cikin mutun.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG