Cutar ciwon daji da akafi sani “Cancer” na cigaba da zama sanadiyar mutuwar mutane da dama a duniya, musamman a kasashen Afrika. Mutane da dama basu sanin wasu daga cikin kananan alamun da ke nuna cewar suna dauke da cutar kansa. Bincike ya nuna cewar milliyoyin mutane a kasashen Afrika na dauke da kwayoyin cutar kansa, batare da sun sani ba.
Amma idan aka kokarta wajen shawo kan cutar da wuri to za’a iya guje ma cutar. Ana dai iya kamuwa da cutar kodai mutun ya gada wajen wani a cikin dangin shi, ko kuma mutun na iya kamuwa da ita a irin yanayin anguwa idan babu tsafta. Kashi talatin na cutar kansa ana iya magance ta, idan anbi hanyoyin kiwon lafiya, wajen cin abubuwa masu gina jiki da kauce ma zama a wurare da basu da tsafta, haka ma da yin rigakafi na duk wata cuta akan kari.
Idan mutane zasu garzaya asibiti don a duba su ko suna dauke da cutar da ake kira HPV da HBV wanda suke cututuka ne masu sa zazzabi nai karfi, a cewar hukumar lafiya ta duniya, za’a iya kauracema cutar baki dayan ta.