Masu iya magana kance “Labarin fuska a tambayi zuciya” Tsare-tsare da kayatarwa na wasu birane a fadin duniya, na daya daga cikin dalilin da yasa aka zabo birane goma 10, a matsayin birane da su kafi kyau da bansha’awa a duniya.
An tabbatar da cewar, masu zanen gidaje da birane a duniya, sunyi amfani da kwakwalwar su fiye da yadda ake tunani, wajen kawatar da wadannan biranen da tsare-tsare masu nagarta. Babban birnin “New York City” shine gari na farko, sai birnin Dubai, haka garin Hong Kong na kasar China, birnin Paris, shima ba’a bar shi a baya ba.
Sai birnin Shanghai, a kasar China, kana garin San Francisco, a jihar California. Garin Cape town, na kasar Afrika ta kudu ya shiga cikin sahu. Garin Vancouver, a kasar Canada ya shiga sahu shi ma, sai garin Budapest. A kasar Hungary, garin Rio De Janeiro, a kasar Brazil shine cikon na goma, a cikin jerin garuruwa da suka fi kayatarwa a duniya.