Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jerin Sunayen Shugabanin Kasashen Duniya Da Suka Fi Yawan Albashi


Ida ana maganar shugabanni da sukafi samu albashi mai yawa a duniya, sai anyi maganar tattalin arzikin kasar. A mafi akasarin kasashen duniya, ‘yan siyasa su sukafi kowa yawan albashi. Amma idan akayi la’akari da haka sai an fara duba yadda tattalin arzikin kasar yake kamin ayi maganar albashin shugabanni ko na ma’aikata a kasar.

Babu wata kasa da ma’aikata suke da albashi da yafi na ‘yan siyasa. A cikin jerin kasashe da shugabannin, su sukafi yawan albashi a duniya. Shugaban kasar Singapore, Mr. Lee Hsien Loong, shine wanda yafi kowa yawan albashi a duniya, yana daukar dallar Amurka milliyan $1.76 a shekara.

Sai shugaban kasar Hong Kong, Mr. Leung Chun-ying, yazo na biyu da yake daukar dallar Amurka $576,000 a shekara. Haka shugaban kasar Switzerland, Mr. Johann N. Schneider-Ammann, wanda ya zo na uku da kuma yake daukar dallar Amurka $460,000 shima a shekara. Na hudu kuwa shine shugaban kasar Amurka, Mr. Barack Obama, da yake daukar kimanin dallar Amurka $400,000 duk a shekara.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG