William Gadoury, wani yaro ne mai shekaru goma sha biyar 15, da haihuwa, yana kan gudanar da wani bincike, da yake nuna cewar, kimanin shekaru 2600 da suka wuce, kamin haihuwar Annabi Isah, anyi wasu mutane da sukayi zamani a wani tsibiri, a yankin kudancin Amurka, tsakanin kasashen Mexico, Guatemala, yanmacin kasar Honduras, El Salvador, da arewacin kasar Belize.
Shi dai wannan yaron, yana amfani da na’urar hangen nesa, inda yaga alamun mutane sun taba zama a yankin, kimanin shekaru dubbai da suka wuce. Hukuma binciken sararin samaniya ta kasar Canada, suna kokarin taimaka ma yaron, don gudanar da binciken, ganin cewar manya-manyan masana basu iya gano kadan daga cikin abun da yaron ya iya ganowa ba.
Yaron ya bayyanar da cewar, kowace kasa a fadin duniya, tana da tauraro a sararin samaniya da yake wakiltar ta. Don haka ya iya gano cewar ita dai wannan kasa da ake kira “Mayans” da ke da tsohon tarihi, mutane sun taba zama a kasar, amma a yanzu babu kowa a yankin.