WASHINGTON, DC —
An gurfanar da wani Bisoye Akinteju, dan shekaru 29, a gaban kotu, a gundumar Badagry dake Lagos, ana zargin sa da laifin satar biskit katan biyu.
Mai gabatar da kara Sufeton ‘yan Sanda Innocent Uko, ya fadawa kotu cewa Akinteju, fizge biskit din ne daga hannun wata mata ‘yar tireda, amma da taimakon jama’a aka kamashi.
A cewar mai gabatar da karar laifin ya sabawa sashe na 245, na dokokin jihar Lagos. Amma wanda ake zargin bai amsa laifin ba, mai lauya mai kare mai laifin ya bukaci kotu da ta bada balinsa.
Alkalin kotun mai shara’a Abiodun Etti, ya bada bailin sa akan kudin Naira dubu hamsin, kuma da shedar cewa mai bailin na biya haraji ajihar Lagos.