Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan-wasa "31" Na Iya Rasa Damar Su A Wasan Olympics 2012!


Tun bayan wasu matsaloli da aka samu a lokacin wasannin Olympics, da aka gudanar shekaru takwas da suka wuce 2008 a Beijing. An fitar da wani rahoto da yake nuna wasu daga cikin ‘yan wasa talatin da daya 31, baza su samu damar shiga cikin gasar wasannin da za’a gabatar a shekarar 2012 a kasar Ingila ba.

A cewar kwamitin kasa-da-kasa dake ladabtar da ‘yan wasa, jiya Talata sun bayyanar da ‘yan wasa talatin da daya daga kasashe goma sha biyu 12, da suka gwabza a wasan da ya gabata, da cewar ba zasu shiga gasa mai zuwa ba. Duk dai da cewar ba’a bayyanar da sunan ‘yan wasan ba.

An zargi ‘yan wasan da shan wasu kwayoyi, a wasan da ya gabata. Duk dai da cewar shaye-shaye na daga cikin laifin da ba’a yafe ma ‘yan wasan, idan aka same su da laifin aikatawa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG