Aure na daya daga cikin al’adu da babu kasa ko kabila da basu yi, sai dai kowannen kasa ko kabila nada yadda suke gudanar da nasu. Wani ango ya saki amaryar shi mintoci kadan bayan gama daura auren su. Dalili kuwa shine a duk lokacin da ake gudanar da shagulgulan auren, amaryar ta dauki lokaci mai tsawo tana waya, da magana da ‘yan uwa da abokan arziki a waya da catin,
Wanda ba taba mijin nata lokaci ba, jim kadan bayan kammala daurin auren, angon ya dauki amaryar, sun tafi wani otel don kara fahimtar juna, sai amaryar ta cigaba da magana da mutane a waya, bata saurari angon nata ba. Tana cikin kokarin amsa mutane da suka aiko mata da sakon murnar auren, sai mijin ranshi ya bace.
A lokacin da angon ya roki amaryar da ta bashi hankalinta, ta bar wannan catin din, sai ranta ya bace. Angon ya tambayi amaryar “Shin wai kawayen ki sun fini ne? Sai tace mishi lallai sun fishi” daga nan sai fada ya kacame a tsakanin su, hakan yasa amaryar ta fita kuma ta nemi da ya bata takardar saki, nan take ya bata.