An bayyanar da wani dan yaro mai shekaru goma sha biyu 12, a matsayin yaron da yafi kaifin basira a fadin duniya. Ya kafa tarihi a duniya, Inda zai zama yaro na farko mai kanana shekaru da shiga jami'a.
Tanishq Abraham, ya samu kamala diploma har guda uku 3, yanzu haka dai manya-manyan jami’o’I guda biyu 2, sun bashi gurbin karatu. Inda yace yana so yayi karatun sanin kwayoyin hallitu kanana “Biomedical Engineering” Yace babban burin shi, shine koda zai kai shekaru goma sha takwas 18, ya mallaki digirin digirgir.
Yaron dai ya fara makarantar gaba da sakandire ne a lokacin da yake dan shekaru bakwai 7, a shekarar da ta gabata ne ya samu kammala diplomomi guda uku a fannoni da-ban da-ban, daya a fannin kimmiyya baki daya “General Science” da na lissafi “Mathmatics” sai daya kuma a fannin “Physical Science” duk a kwaleji daya ta "American River College”