A cikin shekarar da ta gabata, shahararren kamfanin wayoyin sadarwa na Huawei, da ke Najeriya, sun samu babbar nasar. Inda suka samur nau'in wata sabuwar waya G.Power. Dake caji cikin mintoci goma, kuma ta dauki lokaci mai tsawo batare da mutuwar batir ba.
Kamfanin dai ya sake samar da wasu sababbin wayoyi masu rahusa, da suka samu su suna Huawei GR3 da Huawei GR5. Su dai sababbin wayoyin suna da karfin amfani da manhajar 4G, kana an kirkiri wayoyin da wani sinadarin garfe mara fadi, suna da ban sha'awa matuka, kana suna dauke da wasu sababbin manhajoji da ba a ko wace waya ake samun irin su ba.
Su dai wadannan sababbin wayoyin, zasu kara bayyanar da hazakar kamfanin wajen samar da wayoyi masu nagarta da inganci. Suna kuma sa ran idan wadannan wayoyin suka fito, za suyi gogayya da wayoyin kamfanin Samsung, a wajen kudi da abubuwan kayatarwa a cikin su.