Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Nau'o'in Abinci Da Mutane Keci Na Haddasa Warin Baki


Abinci kala bakwai 7, kan sa mutun warin baki, a duk lokacin da mutun yaci abu da ke dauke da wani bangare ko kitsen dabbobi, dai-dai wannan lokacin wasu sinadaran jikin mutun zasu hadu da wasu kemikal na jikin mutun, sai su bada wani launin wari. Haka wasu kayan kanshi da ake sawa a cikin abinci kamar su Kori da jinsin su, suma suna taimakawa.

Yawaita shan kofi shima yana haddasa warin baki, haka idan mutun yana cin abinci da aka saka tafarnuwa, ko albasa, shima ya nasa warin baki harma dai indan mutun bai wanke bakin shiba bayan cin abinci. Ko kuma mutun ya sha ruwa, ko tauna cingam, wanda hakan zai sa bakin mutun ya dinga budewa da kullewa, wajen samun iska da zata kai cikin-cikin mutun.

Haka nama na cikin nau’in abinci da ke haddasa warin baki ga mutun, sai shan wasu abun sha da ba’a inganta su wajen yin su ba, ko amfani da wasu 'ya'yan itatuwa da ba’a gyara suba kamun sarrafa su, shima yana haddasa warin baki. Baki daya ana iya magance duk wannan matsalar, da wanke baki duk bayan cin abinci, ko kuma mutun ya yawaita shanruwa, da amfani da cingam.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG