Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idan Lokaci Ya Wuce Har Abada Ba Zai Dawo Ba


Malama Maryam Abubakar Abba
Malama Maryam Abubakar Abba

A yau dandali ya samu zantawa da Malama Maryam Abubakar Abba, dangane da yadda mata ke mai da hankali wajen hidindimun gida da suka danganci harkokin girke girke a lokacin azumi, su ke kuma mantawa da ibada.

Ta bayyana yadda mace zata tsara aikin abinci da ibada a wannan lokaci tace kamar yadda yakamata a tafiyar da gidan haka yakamata mata su yi amfani da wata na Ramadan wajen kusantar Allah domin samun rahama.

Malam, Maryam, ta kuma jan hankalin mata tana mai cewa “ mu sani cewa rayuwar mu baki daya takaitatciyace “.

Tace idan awa daya ya wuce, rana ta wuce shekara ta wuce har abada ba zasu kuma dawowa ba saboda haka zai dace ayi amfani da wannan damar domin yin biyayya ga Allah.

XS
SM
MD
LG