WASHINGTON, DC —
Hukumar ‘yan Sandan jihar Nasarawa, ta damke wasu matasa a bisa zargin su da amfani da sakamakon makaranta na jabu, wani kuma da satar wayar salula.
Su dai wadannan matasa an damke su a lokaci da ake daukar masu son shiga aikin dan Sanda a garin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.
Kwamishina ‘yan Sandan jihar Alhassan Mamoda, wanda ya bayanawa kamfanin dillacin labarai na Najeriya, wannan labarin yace mutane hudu ne aka kama da sakamakon makaranta na jabu, inda daya cikon na biyar din ake zargin sa da satar wayar hannu .
Yace abin mamaki wanda ke son shiga aikin dan Sanda domin kare lafiya da dukiyar jama’a, ya fara da satar waya a inda ake tantancesu. Ya kuma ja kunnen duk masu muguwar dabia dasu shiga taitayinsu.