WASHINGTON, DC —
A yau mun duba batun nan na yin sahur ne, inda muka zanta da wasu mutane ko shin suna yin sahur inda muka samu sabanin ra'ayoyi daga jama'a, wasu nayi wasu kuwa a'a.
Mun kuma zanta da wani Malam Ali Yunus dagane da muhimmancin yin sahur da ma lokutan da ya dace a yi sahur din.
Yace sahur nada matukar mahimmanci ga mai azumi saboda yana cikin sunnar Manzon Allah (SAW) yayi umarni cewa ayi sahur amma ba tilas bane.
Ya kara da cewa lalle yin sahur akwai albarka aciki kamar yadda ya fada “ kuyi sahur domin akwai albarka aciki kuma yace Allah ta’ala na yin rahama ga masu yi sahur Malaiku suna yin adu’a, ga wanda yake yin sahur, wannan yana nuna mahimmanci yin sahur, babu laifi ga wanda ya dauki azumi baiyi sahur ba sai dai ya bar Sunnah.