Babu wata sana’a da take wulakantacciya, sai dai mutane su wulakanta sana’a, don basu da sha’awar ta. Da yawa mutane kan dauki wasu sana’o’I bada mutunci ba. Wasu kuwa sukan girmama sana’a kowace irin, don su wucema rayuwar su abun takaci.
Wani matashi mai sana’ar kabu-kabu, a babban birnin Lagos, ya maida Keken NAPEP din shi, wata babbar mota. Mutane da dama nata maganar yadda wannan matashin ya dauki sana’ar shi babu raini ko wulakanci.
A cikin Keken nashi akwai na’urar kallon fim, da fanka don nishadantar da kwastomomin shi. Mutane da dama sun bayyana wannan matasahi da wannan yunkuri nashi, na nuna sana’ar shi tana da muhimanci.
Da kara jawo hankalin sauran al’uma da su dauki sana’a kowace da matukar muhimanci. Kowace sana'a mutun na iya maidata sana'ar da tafi kowace kyau da tsafta, idan yayi la'akari da yadda ake gudanar da ita a kasashen da suka cigaba, daga nan sai mutun ya zama wani abu.