Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kashe Matarsa A Kan Naira 100


Rundunar ‘yan Sandan jihar Imo, ta damke wani mutun dan shekaru 36, mai suna Onyekachi Anele, wanda ya mari matar sa kuma marin yayi sanadiyar mutuwar ta.

Shi dai Anele, da matar sa mai suna Chikodi, sun samu wata ‘yar rashin jituwane, wace ta kai ga Anele, ya mari matar tashi ita kuwa ta rama sai ya fusata ya sake kwashe ta da mari nan take ta sume daga nan tace ga garin ku nan.

Jaridar Vanguard, ta ruwaitu cewa ma’auratan biyu na zaune ne a Obiniezena, a karamar hukumar Owerri ta arewa, kuma suna da ‘ya’ya biyu tare.

Dalilin rashin jituwar dai shine cewa matar shi ta yi masa rashin kunya ne akan Naira 100,

Da yake bayani Anele, yace yana son matar sa kuma bashi da niyyar kashe ta amma rashin hakuri ne ya jawo duk wanna.

Shugaban kungiyar mata ta Women Network ta jihar Imo, Dr. Joyce Soroibe, ta bukaci da hukumar ‘yan Sanda ta hanzarta bincike da tabbatar da cewa anyi adalci a shara’ar.

Tace idan aka yi masa hukunci da ya dace zai zama ishara ga mazaje masu dabi’ar dukan matansu .

XS
SM
MD
LG