A makon da ya gabata mun tattauna ne akan samartaka a lokacin ramadana, kuma tambayar da muka yi wa yawancin samari da 'yan mata ita ce, ko suna ganawa da juna a wannan lokaci na ibada, sa'annan ya sha'anin amfani da wayar hannu da suka saba hira wadda harma a wasu lokuta sukan aikawa juna hotuna!
Yawancin 'yan matan sun dora duk wani laifi ne akan samari, a yayinda su kuma samarin suka nuna cewa "idan bera yana da sata, to daudawa ma nada wari" dan haka laifin ya rataya akan su duka.
Duk da cewa lokaci ne na ibada, amma yawancin samarin da muka yi hira da su sun bayyana mana cewa suna ganawa fiye da lokacin da ba'a azumi musamman ganin yadda suke fita zuwa karatu ko masallaci ko wurin tafsir a kowane dare.
Wannan bayani ya ja hankalin jama'a da dama domin kuwa a cewar magabata, haka bai dace ba domin kuwa ba da sanin iyaye samari da 'yan mata ke haduwa wuri Tafsir ko masallaci ba domin kuwa iyaye sun tura su ne domin ibada badan haduwa da samari ba.
Malamai da iyaye sun yi kira ga sauran al'uma da su rika sa ido akan 'ya'yan su domin tabbatar da cewa suna aikata ayyukan da suka dace domin a cewar su yaro yaro ne, dole sai da kulawa, da bada shawarwari domin samun makoma mai kyau a rayuwa.