Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saida Ta Boye Jikokinta A Mota Sa'annan Ta Harbe Mahaifiyar Su


Mujallar kasar Amurka Washington Post ta wallafa labarin wata mata mai shekaru sittin da uku da haihuwa ta hallaka surukarta ta wajan harbin ta da bindiga bayan ta kwashe ‘ya’yan matar wato jikokinta ta kai su cikin mota sa'annan ta koma ta harbe uwar yaran a cewar jami’in dan’sanda mai mukamin saja Mr Dana Pierce.

Jami’in ya kara da cewa yaran na cikin mota ne a yayin da tayi harbin amma yaran basu san mahaifiyar su aka hallaka ba, Dana ya kara da cewa tsohuwar mai suna Elizabeth ta harbe surukar ta mai shekaru talatin da biyar da haihuwa ne domin tana kan kokarin raba aurenta da mijinta.

Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu ana kan bincike domin gano dai dai lokacin da lamarin ya faru domin a cewar jami’in dan’sandan, bincike ya nuna cewa bayan ta harbe surukar tata, tsohuwar ta kira dan nata wanda ya garzaya ya sameta a gidan daga bisani ya kira wayar neman daukin gaggawa ta jami’an tsaro wato 911.

A halin da ake ciki dai yanzu matar mai shekaru sittin da uku da haihuwa na hannun jami'an tsaro, amma har yanzu ba’a da tabbacin ko ta dauki lauyan da zai kare ta ba kokuma a’a.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG