A yayin da aka shiga gomar karshen na azumin watan Ramadana , a yau dandali ya samu zantawa da limamin masallacin Usman Bin Uffan dake Kofar Gadon kaya a Kano, inda ya ke bayyana mana muhimmancin daren lailatul Qadr da lokutan da ake fatan dace da wannan dare.
Ya kuma ja hankali matasa masu dabi'un zuwa sallar tuhajjud masu fesa kwaliya domin samun samari da cewar wannan dabi'a ta su ba daidai bane.
Ya kara da cewa yakamata matasa su san mauhimmacin zuwa tahajjud cewa ana zuwa ibadah ne ba wuri na baje koli na yin kwaliya da wargi da kuma bata lokaci ba, idan har mutun ba zai tsaya ya yi ibadah ba gwamma ya kwanta yayi barci shi yafi masa alheri fiye da ya sabawa Allah.
Inda ya ke cewa wannan lokaci ne da yakamata jama’a su maida hankali domin samun rahamar Allah a cikin wannan wata mai alfarma kamar yadda Allah yayi alkawari rahamarsa ga duk wanda yayi tsayiwar dare.