Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasan Cewa Lionel Messi Ya Bugawa Kasarsa Wasa Sau 113


Kamar yadda wasannin cin kofin nahiyar Amurka COPA America ya tashi, kasar Chile ta kare kambin ta, inda ta sami nasarar lashe gasar ta bana bayan da ta sami galaba akan kungiyar kwallon kafa ta Argentina bayan shafe mintuna 120 ana fafatawa babu wanda ya sami zura kwallo wanda daga karshe yasa aka yi bugun kifa daya kwala ko fenariti.

Kasar Chile ta jefa kwallaye guda hudu, yayin da takwarar tata ta jefa guda biyu, wannan dai za’a iya cewa tarihi ne ya maimaita kansa, domin kuwa kasashen biyu ne suka fafata a karshen wasan na kakar bara.

Shahararren dan wasan Argentina Lionel Messi na daya daga cikin ‘yan wasan da ya gaza jefa kwallo a bugun fenaritin da kungiyoyin wasan suka yi daga karshe.

A nan take ne dan wasan ya bayyana aniyarsa ta daina bugawa kungiyar kwallon kasar wasa. Messi dan shekaru 29 da haihuwa ya lashe kyautar dan kwallon duniya har sau biyar, ya kuma daga kofin Laliga takwas, da kofin zakarun Turai hudu a kungiyar Barcelona ta kasar Spain.

Wannan shine karo na biyu da dan wasan ya sha kashi a hannun kungiyar ‘yan wasan Chile, dan wasan ya bugawa kasarsa wasanni har sau 113, tun daga shekarar 2005.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG