A yayin da azumin watan Ramadana ya zo gangara , a yau mun yi duba ne dangane da Zakatul-fitr ,in da muka sami zantawa da Malam Ahmad Tijjani Mijinyawa dangane da muhimmancin zakatul-fitr a musulunci .
Malamin ya ce zakatul fitr zakka ce da ake yin ta bayan an kamala Azumin watan Ramadan, sunnah ce ga duk wanda ya sami iko amma dai tana kan duk wanda ya sami dama matukar dai shara’a ta hau kansa na miji ko mace.
Yana mai cewa ana iya fitarwa kwanaki biyu kafin aje idi kuma wanda bashi da aure na fitar da zakatul-fitr domin Sunnah ce mai karfi.
Malam Mijinyawa, ya kara da cewa shara’a ta nuna cewa rukunin masu rauni ne ya wajaba a baiwa zakatul-fitr, kuma wadanda su fitar sun amsa , ka'idojin da sharrudan da Allah ya shinfida akan zakatul-fitr wanda shi yasan irin ladar da ya dace ga wanda ya aiwatar.