A karon farko hukumar binciken sararrin samaniya NASA, ta fitar da bidiyon yanayin duniyar watan “Mars” wanda mutunmutumin “Curiosity Rover” ya dauka tun bayan tura shi duniyar da akayi shekaru biyar da suka wuce.
Bidiyon dai ya nuna zagayen duniyar na murabba’in 360, wanda aka dauka a ranar biyar ga watan Augusta. Babban abun sha’awa da hoton bidiyon shine, yadda ya bayyanar da tsarin cikin duniyar ba waje ne da yake a bude ba, yana da tudu da kwari kamar yadda wannan duniyar take.
Mutunmutumin yayi yayo matuka cikin duniyar, duk da wasu yan matsaloli da ya fuskanta, na tsallake wasu tudu da gangara. Haka da wasu abubuwa masu kama da duwatsu, sun shigar mishi gaba sau da yawa. Hukumar ta NASA, na kokarin ganin yadda za suyi amfani da mutunmutumin, don kara fahimtar hallitun da suke cikin duniyar ta wata.