Kimanin nan da ‘yan makonni kadan, hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Amurka NASA, zasu kaddamar da wani sabon jirgi mai yawo a cikin sararrin samaniya, wanda akayi ma lakani da “OSIRIS-REx”
Shi dai wannan jirgin, zai tafi cikin sararrin samaniya ne, don yawon bude ido da kara bayyanar da yadda ake gudanar da rayuwa a cikin duniyar sama. Ana kuma sa ran zai kara bincike akan duwatsu da suke fitowa daga duniya “Bennu” wanda ake sa ran suke dauke da wani sinadari, dake tallafawa rayuwar dan’adam.
Binciken zai kara bayyanar da yadda rayuwar wata da taurari suke, haka da yadda ake gudanar da rayuwa a wata duniya, bayaga irin duniyar da mutane ke ciki. A na dai sa ran idan Allah ya kai rai, ranar 8 ga watan Satunba za’a harba wannan jirgin.
Shugaban binciken Gordon Johnston, ya bayyanar da cewar za’a tura wannan jirgin, don gudanar da bincike ne wanda ake sa ran zai kwashe tsawon shekaru biyu kamin samun sakamako.
Sakamakon da ake sa ran samu shine, taya mutane za suje duniyar wata don yin wasa, irin yadda ake gabatar da wasa a doron kasa. Wasa irin wanda ya shafi yara ba kawai sai manyan mutane ba.