A wani bincike da aka gudanar, da ya bayyanar da wasu abubuwa, da basu kamata mutun yayi suba, a lokacin da yake cikin jirgin sama, jirgin kasa da motar haya. Kada mutun yayi tafiya batare da takalmi ba, ko kuma ya zauna a wajen da bashi da tsafta.
Sau da yawa mutane kanyi amai, ko zubar jini, wanda ba’a cika daukar matakan da suka kamata, wajen tsaftace kayan da mutane kanyi amfani da su. Haka mutane su lura da yanayi kamin su ci wani abu, a yayin da suke cikin abun hawa na kasuwa, wasu kananan cututtuka kan makale a inda mutun bai zata ba, don haka riga kafi yafi magani.
Haka yin bacci a cikin jirgi, ko motar haya, kan iya haifar da wasu cututtuka idan ba’a samun iska mai inganci a cikin jama’a. Saka kaya masu rufe jiki na da mahimanci kwarai, da gaske don guje ma shafar fatar jikin mutun, da kujera ko karfe dake dauke da wasu kwayoyin cututtuka da ido baya gani.