Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Alhamis Da Safe Wasu Biranen Najeriya Za Su Ga Husufin Rana


Babban daraktan ma’aikatar binciken yanayi Farfesa Babatunde dake jihar Kogi a wata hira da kamfanin dillancin labarum Najeriya ya bayyana cewa da dama daga cikin jihohin Najeriya zasu fuskanci husufin rana yau talata 1 ga watan Satumbar wannan shekara da muke ciki.

Farfesan ya bayyana hakanne jiya laraba a yayin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai a Abuja babban birnin kasar,husufin zai fara daga karfe 7:13am na safiyar alhamis.

A cewar sa, yankin Fatakwal ne zaifi ganin wannan Husufi wanda zai dauki kusan mintuna uku da dakika shidda, kamar yadda ya saba afkuwa a yankin gabashin nahiyar Afirka.

Ya kuma kara da cewa a jihar Sokoto ma za’a ga husufin to amma sai dai bazai dauki lokaci mai tsawo kamar na fatakwal ba, haka kuma wasu sauran biranen Najeriyar amma ya danganta da lokacin.

Shi dai Husufin rana kan faru ne a yayin da wata kan yiwa rana inuwa, wanda ke haifar da inuwa da kuma dakushe hasken rana na dan wani loaci.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG