WASHINGTON D.C —
Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa na Flying Eagles, Samson Siasia, ya nuna rashin jindadinsa ga Attajiran Najeriya, ganin yadda suka juyamasu baya a lokacin da suke Atlanta, ta kasar Amurka suke shirye shiryen zuwa gasar Olympic a kasar Brazil.
Ya ce a lokacin da suke fama da rashin kudi, ya tuno da wani likita dan kasar Japan, Katsuya Takasu wanda ya taimakawa kungiyar da tsabar kudi dalar Amurka dubu dari ukku da tasa’in.
Siasia ya kara da cewa su kuwa masu arzikin Najeriya, babu wanda Yayi tunanin ko kwandala, duk da ya kasance cewa sun sami labarin halin da ‘yan kwallon ke ciki, yana mai cewa Katsuya Takasu, lalle ya nuna shi mutun ne kuma muna godiya.