Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Gungun Wasu Masu Sata Da Sayar Da Yara


Hukumar jami’an tsaro masu farin kaya watau DSS, shiyar jihar Benue, ta damke wasu mutane da ake zargin sun shahara wajan satar da sayar da yara inda aka nuna su ga jama’a a jihar.

Wadanda aka kama sun hada da Adejo Ogiri,wanda kuma ake kira da Okala, Affonne Nwokocha, dan karamar hukumar Umuahia, ta kudu a jihar Abia, da Ezekiel da kuma mai dakinsa Amarachi.

Nwokocha, wanda ya amsa laifin san a sayar da yaran shi kuwa Okala cewa yayi ya sato yara hudu wanda daga bisani ya mika su ga wani matukin mota Ezekiel daga jihar Imo.

Adejo, yace duk lokacin da ya sato yaro daga kowane bangaren jihar sai ya mika shi ga Ezekiel, wanda shi kuma ya mikawa mai dakinsa Amarachi wanda shahara wajan amsan yaran da aka sato.

Ya kara da cewa yaro da ya sato dubu ya cika sunansa Miracle Jacub, wanda aka baya shi Naira miliyan daya akai, an kuma ceto wasu yara daga hannun wadanna mugaye .

Yaran da aka ceto sun hada da Emmanuel Abedi, Favor Oleka, James Adanu da Joseph Aboje.

XS
SM
MD
LG