Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wani Mai Kamfanin Jarirai Da Mai Dakinsa


Rundunar ‘yan Sandan jihar Abia, ta cafke wasu matasan ‘yan mata Esther Odum da Ebere Ejimadu da suke niyyar sayarda ‘ya’yan jikinsu.Kwamishinar ‘yan Sandan jihar Leye Oyebade,wanda ya gabatar da ‘yan mata ga manema labarai,ya ce an damke ‘yan matan ne tare da wata mai suna Oluchi, matar mai kamfanin jariran inda suke fatan haihuwar jariran wanda kuma daga bisani zasu sayarda jariran.

Kwamishina, ya ce rundunar ta sami tsegumi ne cewar Ifeanyi Agbasonu da mai dakinsa Oluchi, suna da kamfanin jarirai a wani gida mai lamba 2, Bridget Road Aba, wanda a lokacin

Da ‘yan Sanda suka kai farmaki suka yi nasarar cafke wandannan ‘yan mata masu juna biyu da suke da niyyar sayarda su idan su haihu.

‘Yan matan biyu sun musata zargin cewa suna da wata niyya na sayarda jariran su idan su haihu, duk sun ce sunje neman magani a wuri Ifeanyi wanda yake mai maganin gargajiya ne, Odum dai ‘yar asalin jihar Imo ce ita kuwa Ejimadu, ta ce daga Fatakwul, ta zo.

XS
SM
MD
LG