WASHINGTON, DC —
A ci gaba da wasan neman gasar cin kofin kwallon na duniya na shekara 2018, wanda za’a yi a kasar Rasha, a satin da ta wuce kasar Argentina, ta sami nasara akan kasar Uruguay, da ci daya mai banhaushe.
Slovakia, ta sha kashi a hannun Ingila, ita ma da ci daya mai banhaushe, yayinda San Marino, ta sha kashi a hannun Azerbaijan, da ci daya da babu.
Denmark ta sami nasara akan kasar Armenia ita ma da kwallo daya da nema, yayin da Kazakhstan suka tashi kunnen doki da kasar Holland.