Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya bayan sunan dan wasan Super Eagles na Najeriya, Kelechi Iheanacho, a matsayin wanda zai maye gurbin Sergio Aguero, a babban wasan da zasu fafata da kungiyar Manchester United, ranar 10, ga wannan watan na Satumba, a gasar firimiya lig, na bana.
Shi dai Sergio Aguero, an dakatar da shine bisa laifin cewa ya naushi dan wasan West Ham a yayin wasansu da suka fafata na firimiya lig a makon da ya gabata, an dai dakatar da Sergio Aguero ne daga buga wasani ukku.
A wani labarin kuma kungiyar alkalan wasan kwallon kafga na kasar Ingila, ta bayana sunan Mark, a matsayin alkalin wasan da zai yi alkalancin wasan da za’a buga tsakanin Manchester Unitedf da Manchester City, a Old Strafford, wasan da ke sa ran cewa zai dauke hankalin masoya wasan kwallon kafa.