WASHINGTON, DC —
A gasar firimiya lig, da ake shirin yin a sati na hudu, hukumar tsaro na ‘yan Sanda dake kasar Ingila, ta bayana cewa zata bada ‘yan Sanda har dari hudu a filin wasan da za’a fafata tsakanin Manchester City da Manchester United.
Wanna wasan ana ganin cewa zai dauke hankalin masoya wasan kwallon kafa, a duniya.
Wadannan kungiyoyi biyu sune suka fi kowace kungiya baiwa hukumar tsaron Ingila kudi domin kare lafiya ‘yan wasa da ‘yan kallo a yayin wasan.