WASHINGTON, DC —
Wani yaro dan shekaru goma, mai suna Daniel, ya gamu da ajalinsa yayin da suke ninkaya a wani katafaren magudanar ruwa da shi da abokansa a Calabar, jihar Cross River.
Jaridar Vanguard, ta ruwaito cewa abokan shi wannan yaro mai suna Daniel, sun dauki gawar abokinsu suka kewaye wasu titunan garin Calabar, kafin a binne.
A cewar daya daga cikin abokansa mai suna Effiong, ya ce inda suke ninkayar wanda ake kira da katon lambatu ruwan sun karu sosai, gashi kuma Daniel bai iya iyo ba.
Daga bisani dai an gai gawar unguwar Bagobiri, inda ya kasance inda suke zaune, inda kuma aka yi masa janaiza.