Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Akwa Ibom Ta Agazawa Super Eagles


Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta yabawa gwamnatin jihar Akwa Ibom, bisa kokarin da tayi na daukar nauyin wasan da Najeriya tayi da kasar Tanzania, na neman shiga cin kofin Afirka, na shekaran 2017, inda Najeriya ta sami nasara akan da ci daya mai banhaushe.

Hukumar ta NFF, ta bayana haka ne ta bakin sakataren ta Dr. Muhammad Sanusi.

Hari la yau hukumar ta tabo batun kudin da gwamnatin jihar Akwa Ibom, ta bayar bayan kammala wasan da Najeriya, tayi da kasar Tanzania, har dalar Amurka, dubu ashirin da biyar ($25,000) kimanin Naira miliyan goma kudin Najeriya.

Jami’in watsa labarai na hukumar ta NFF, Ademola Oladele, yace hukumar zata yi amfani da kudaden ne wajan biyan alwus alwus din ‘yan wasan.

Ya kara da cewa asalin kudaden da aka ware domin a biya alawus din ‘yan wasan an shirya shine bayan ‘yan wasan sun dawo dag wasan su da Zambia wasan da zasu buga a watan Oktoba inda zasu fafata a gasar neman gurbi a gasar cin kofin duniya na shekarar 2018.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00

XS
SM
MD
LG