Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Damke Wani Mai Fataucin 'Yan Mata


Kungiyar ‘yan sintiri, ta jihar Benue, ta damke wani mutun mai suna Israel Lame, da ake zargin cewa mai fastauci mutane ne.

Shi dai Israel Lame, an damke shine a tashar mota a lokacin da yake kokarin tserewa da wasu ‘yan mata biyu a garin Gboko, dake jihar ta Benue, akan hanyar su ta zuwa Legas.

Kakakin ‘yan Sandan jihar ta Benue, ASP Moses Yamu, a lokacin da yake gabatar da Lame, da wasu masu laifi goma sha biyar ga manema labarai a hedkwatar ‘yan Sandan dake Gboko, ya ce an damke shine bayan da wani ya tseguntawa hukuma.

Lame, wanda yake da takardan zama dan kasar Najeriya, da ta Kamaru, ya ce shi dan jihar Cross River, ne.

Kakakin ‘yan Sandan yace Israel Lame, ya shahara wajen fataucin ‘yan mata, zuwa kasar Burkina Faso, ‘yan matan dake tare dashi a lokacin da aka damke shi sunan su Timia Daasha, yar shekaru 20, ‘yar asalin jihar Filato, da Joy Gideon, ‘yar shekaru 24, daga jihar Benue.

XS
SM
MD
LG