Rundunar ‘yan Sandan jihar Legas, ta damke wani direba matashi dan shekaru ashirin da biyar da haihuwa mai suna Mayowa Adenuga, a bisa zargin satar kudin mai gidansa fiye da Naira Miliyan biyu da dubu dari bakwai (2,700,000).
Shi dai wannan matashi ya sace katin bankin mai gidansa ne a cikin mota ya bayan kwanaki ukku, da mai gidan mai suna Farfesa, Simbo Banjoko, wanda yake malami ne a jami’ar, Legas, bai nemi katin ba sai ya kaiwa abokinsa Adewale Opeyemi, ya boye masa cewa katin na ‘yar uwarsa ne, koda yake an hada har da wani abokin su mai suna Jeremiah Iyitoye, suke hannun ‘yan Sanda.
A cewar jaridar Punch, Mayowa, kwararre ne a harkar kwamfuta, wanda yayi amfani da ilimisa na wannan naura inda ya bude katin, ya kuma dakile lambar wayar mai gidansa ta inda ba zai ga duk wata siyayya da aka yi da katin ba.
A cewar rahoton shi dai Mayowa, ya fitar Naira dubu dari biyu (200,000) daga ajiyar bankin mai gidan nasa, ya kuma sayi wayar hannun ta iPhone guda hudu da kudin su ya kama dubu dari hudu da tasa’in da biyar (495,000) da Kwamfutar Macbook, wanda kudinta ya kasance Naira dubu dari hudu da goma sha biyar (415,000).
Sauran kayayyakin da ya saya sun hada da agogunan hannu guda goma da wayar hannu ta Blackberry da zobe, jimilar kudaden da ya kashe dai Naira miliyan biyu da dubu dari bakwai da ashirin da takwas da dari biyu da hamsin da biyar (2,728.255).