WASHINGTON, DC —
Sabon mai horar da ‘yan wasan Super Eagles, Gernot Rohr, ya ce gidan da aka bashi domin wanda ke matsayin muhallinsa a Abuja, yayi masa girma.
Gernot Rohr, dan shekaru sittin da ukku, alokacin da yaje ganin gidan da hukumar kwallon kafa ta Najeriya, watau, NFF, ta karbin hayan sa domin mai horar da ‘yan wasan, a unguwat jabi, a Abuja, ya ce zai bukaci gidan da bai kai girman wannan ba.
A bisa yarjejeniyar dake tsakanin hukumar da mai horar da ‘yan wasan akwai batun muhalli da kuma mota.
Za dai a biya dan kasar Jamus, din dalar Amurka dubu arba’in da bakwai (47,000) a wata.