Alamu dai na nuni da cewar dan wasan kwallon kafar kungiyar kasar Germany, Vincent Enyeama, tsohon dan wasan klob din Super Eagle zai dawo gida. A cewar shi idan har shugaban klob din zai aminta Mr. Gernot.
A cewar Mr. Gernot Rohr, idan har ‘yan wasan su, suka samu nasarar lashe wasan da zai basu damar shiga gasar zakaru na shekarar 2018 na kungiyar kwallon kafar duniya FIFA. Tsohon mai tsaron gidan kungiyar Vincent, zai dawo da karfin shi.
Koci din dai ya bayyanar da cewar, yayi kokari matuka wajen ganin ya jawo ra’ayin mai tsaron gidan, don ya dawo ya buga ma kasar shi wasa, ganin cewar zai iya zama mai tsaron gida, da zai kafa tarihi a duniyar kwallon kafa, musamman a kasashen Afrika.
Dama dai mai tsaron gidan ya bar kungiyar ne, a sanadiyar wata sa’insa da su kayi da tsohon shugaban kundiyar Sunday Oluseh. Anasa ran idan ya aminta da dawo, kungiyar ta Super Eagle, zasu iya zama gagara misali ba kawai a kasashen Afrika ba, harma da duniya baki daya.