Wani likita dan Najeriya mai suna Dr Oluyimka Olutoye, tare da abokin aikinsa Dr Darel Cass, a asibitin yara dake jihar Texas ta kasar Amurka ya yi wa wata ‘yar tayi mai sati 23, a cikin uwar ta aikin fida, kana ya mayar da ita cikin mahaifiyar ta, bayan sati na 36, aka haife ta cikin koshin lafiya.
Yayin da mahaifiyar jinjirar mai suna Margaret Boemer, ta je ziyarar awon ciki kamar yadda mata masu juna biyu suka saba a sati na goma sha shidda, likitan ya duba ta inda ya lura da cewar wani abu na faruwa da ‘yar tayin dake cikin Margret.
A cewar Matar, lamarin ya saka ta cikin damuwa da kaduwa bayan likitan ya bayyana mata da mai gidan ta cewar akwai matsala tattare da ‘yar tayin dake cikinta, musamman yadda likitan ya bayyana sunan matsalar mai tsayin gaske da ba kowa yasani ko taba jin sunan irin wannan cut aba.
Rahotanni sun bayyana cewa akasarin irin wannan matsala takan kama jarirai mata fiye da maza, wato akan sami guda daya a cikin dubu talatin da biyar na sababbin jarirai da aka Haifa, kuma yakan kama ‘yan tayi ne a cikin mahaifa tun kafin a haife su.
Likitan ya bayyana cewa yawanci wannan cuta kan girma ne a cikin mahaifa inda take hana gudanar isashshen jini a jikin dan tayi wanda ke haddasa tsayawar bugun zuciyar jariri sakamakon rarrabuwar gudanar jinin tsakanin dan tayi da cutar mai suna Sacrococcygeal teratoma a turance.
Likitoci da dama sun ba Margaret shawarwarin zubar da cikin tunda a cewar su, koda ta bar cikin daga karshe bazai rayu ba gannin yadda cutar ke lakume duk jinin da yakamata dan tayi ya samu a lokacin da yake girma a cikin mahaifar uwar sa.
Dr Oluyinka ya bayyana cewa sun ba Margret zabi a lokacin da cikin yake da sati ashirin da uku da kwanaki biyar, kuma ta amince, yayin da kwayar halittar cutar ta kusa fin girman ‘yar tayin.
Wannan abin al’ajabi ya faru ne bayan likitan wanda asalinsa dan Najeriya ne da abokin aikinsa suka kwashe awoyi biyar suka ciro ‘yar tayin mai sati ashirin da uku a cikin mahaifa, sa’an nan suka cire wannan cuta daga jikin ta kuma suka mayar da ita cikin mahaifar uwar ta wadda daga karshe ta warke a cikin mahaifar kuma bayan sati na 36 aka haife ta cikin koshin lafiya.