Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Super Eagles Odion Ighalo Na Fuskantar Hukuncin Daurin Shekaru 2


Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Odion Ighalo na fuskantar hukuncin daurin shekaru biyu a sakamakon zarginsa da aka yi na aikata laifin cin hanci da rashawa a yayin da yake takawa kungiyar kwallon kafa ta kasar Spaniya leda.

Mujallar Marca, ta kasar Spaniya ta wallafa cewa ofishin babban lauya mai gabatar da kara na lardin Granada na kasar ya bukaci a daure dan wasan kwallon kafar har na tswon shekaru biyu da kuma cinsa tarar zunzurutun kudi Euro dubu uku, a sakamakon samun Ighaho da tsohon abokin aikinsa Diego Bounanotte, da kuma wasu mutane 93, da laifin bada cin hanci da rashawa a lokacin da suke kokarin zana jarabawar samun lasisin tuki.

A cewar rahoton mai shigar da kara, a shekarar 2012/2013, dan wasan da sauran wadanda kotun ke tuhuma sun yi hayar wasu daban wadanda suka zana masu jarabawar samun lasisin tuki a kasar. bincike ya nuna cewar an goge duk kurakuran da aka tafka akan takardar jarabawar wadda keda alaka da rashin iya rubuta sunan dan wasan daidai, kuma ana zargin dan wasan ya biya kudi tsakanin Euro 1,500, zuwa 2,500 domin a zana masa jarabawar.

Biyo bayan lamarin, mai shari’ar ya sami dan wasan na kungiyar Super Eagles da laifin yin karya akan takardu na musamman, ana kyautata zaton za’a gurfanar da Ighalo gaban kotu a bainar jama’a inda za’a tuhume shi.

Haka kuma a farkon wannan makonne wata kotun majistire dake birnin Westminster, ta bada sammacin gurfanar da wani tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na kungiyar Super Eagles, Efetobore da ‘yan uwansa , Bright me shekaru 50, da Samuel me shekaru 37, da Stephen me shekaru 42, domin zargin su da aikata laifin zamba cikin aminci.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG