Babu wani mai kudi da aka haife shi ko ita da kudi, ko kuma iyayen su sun haife su da cewar sai sun zama masu kudi. Mafi akasarin masu kudi a duniya, idan aka duba tarihin rayuwar su, za’a ga cewar sun kasance mutane masu hangen nesa da godiya ga irin abun da suke da shi ne.
Amma haka bai hana su kallon wasu da suka samu nasara a rayuwa ba, don koyi da irin hanyoyin da suka bi na samun nasara, wajen zama abun da suka zama. Wasu kadan daga cikin sharudda da duk wanda bai kokarta ba wajen bin suba, zai yi wuya mutun ya zama mai kudi a duniya.
Yana da matukar mahimacin mutun ya dauki sana’ar da yake sha’awar yi, a lokacin da yake kokarin tsara ma kanshi abun yi, kada ya dauka saboda wani ya dauka kuma yayi nasara, shima zaiyi. Haka kada mutun yaji tsoron kowace irin sana’a ko aiki, domin kuwa duk sana’a da aiki suna tare da irin nasu nau'u'u'kan hadduran.
Tsimi da tanadi, suna daya daga cikin sharuddan tara abun duniya, kada kuma mutun ya dauki rayuwar karya, wajen siyan abubuwa da sukafi karfin nema da samun mutun. Daukar bashi babbar matsala ce, musamman ga dan kasuwa ko ma’aikaci da ke neman tara abun kan su.
Mutunta lafiya uwar jiki, hanyace da mutun zai inganta neman shi, don idan mutun yana ci da sha wadanda zasu taimakama lafiyar shi, hakan zai bashi damar tanada abun da yake da. Kasafi da tsari kamin aiwatar da wasu saye-saye yana da mahimanci, don bama abubuwa da su kafi mahimanci kulawa ta musamman.
A karshe, biyan duk wani hakki da ya rataya a kan mutun, a lokacin da ya kamata walau na mahallicci, ko na tsarin kasa, sai kyautata ma duk wani da ya biyo ta hanyar sana’ar ka, ko aikin da kakeyi don dogaro da kai.