Esther Ruby Daniel, ‘yar Najeriya ce, mai shekaru goma sha bakwai 17, da haihuwa. Wadda take karatu a jami’ar “Amity” a kasar India. Yanzu haka dai wannan matashiyar, ta kafa tarihi a tsohuwar Jami’ar Amity. Inda ta samu lambar yabo da ba’a taba samun mutun daya da ya samu kyaututukan da ta samu ba.
Matashiyar na aji biyu a jami’ar, inda take karatun shari’a “Law” ‘yar asalin jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya ce, a cikin wata daya, ta samu damar lashe kyautar Tagulla, a gasar dalibai masu karatun shari'a a baki daya kasar india. Sai kuma kyautar Zinariya, da Azurfa na masu tseren mitoci dari biyu 200.
Sai ranar 5 ga watan Oktoba, inda ta kara samun kyautar Zinariya, a wasan tsalle, kana ranar 6 duk a cikin watan da ya gabata, ta sake samun Zinariya tseren mita dari 100, sai ranar 14 ga watan Oktoba, shima ta sake samun Azurfa.
Ranar ashirin da yada 21, kuwa ta samu nasarar samun kyuatar kofi, wadannan nasararorin da ta samu suna da alaka da irin kokarin ta a wajen wasannin motsa jiki.
A zantawa da manema labarai da tayi, ta bayyanar da cewar wannan kadan ma daga cikin irin kokarin ta kenan, don tana sa ran kamun ta kammala karatun ta na digiri, sai ta samar ma kasar ta Najeriya, suna a idon duniya.
Mahaifin yarinyar Mr. Daniel Thomas, ya kara jawo hankalin matasa, da a duk inda suke, su dinga tunawa da kasar su, don kokarin ganin sunan su ya shiga cikin tarihin kasar su, tun da kuruciyar su. Yana alfahari da ‘yar shi da irin kokarin ta.