Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Wanda Ya Tsira Daga Kutsen Satar Bayanai A Shafin Twitter


Wata kungiyar masu kutse a yanar gizo dake kiran kansu da suna OurMine, tace tana kaiwa fitattun kamfanoni hari a shafikansu na kafofin sadarwa domin ta tallata aikinta na tsaro.

Kungiyar OurMine dai ta kai wa shafukan kamfanoni da suka hada da babban kamfanin nan dake yin wasannin video game mai suna Marvel Hero da The Avengers da Captain America da kuma Ant-Man, hari inda suka kafe wani sako iri ‘daya a duk shafukan wanda ke cewa “Sannu, OurMine ne, karka damu muna gwajin tsaron ka ne, a tuntubemu mu taimaka maka wajen tsaro.”

Biyo bayan wannna sako da suke kafewa a duk shafin da suka yiwa kutse, suna kuma barin adireshinsu na email domin a tuntubesu.

Ita dai wannan kungiya dake ikirari da suna OurMine, akan shafinta na yanar gizo tana yin tallar bayar da tsaro ga shafukan yanar gizo da kuma shafukan dandalin sada zumunci musamman ga kamfanoni ko wasu fitattun mutane, akan farashin Dalar Amurka 30 ga shafukan sadarwa, ko shufukan yanar gizo na kamfanoni akan kudi da ya kai Dala dubu ‘daya zuwa Dala dubu biyar.

A farkon wannan shekara ne dai mujallar fasaha ta TechCrunch ta fitar da rahotan cewa wasu matasa uku ne suka kafa wannan kungiya, matasan da mujallar bata bayyana ko su waye ba. cikin manyan sunayen da kungiyar tayiwa kutse har da shugaban Facebook Mark Zuckerberg da shugaban Google Sundar Pichai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:30 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG