Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Mata Mashaya, Ya Ribanya Na Maza Mashaya A Fadin Duniya!


Shaye-Shaye
Shaye-Shaye

Wani sabon rahoto na nuni da cewar, an samu karin yawan mata dake mutuwa sanadiyar shaye-shaye a fadin duniya. Wanda mata kalilan ne kan samu kulawa da ta dace, idan aka hada da adadin maza da kan samu kulawa a fagen shaye-shaye.

Rahoton karshen shekara na hukumar kasa-da-kasa don yaki da kwayoyin Narcotic, sun bayyanar da cewar, gwamnatoci a duniya basu kulawa da wannan bangaren yadda ya kamata, musamman idan akayi la’akari da yadda yawan mata ke karuwa a wajen shaye-shaye.

Hukumar dai na bibiya ga tsarin majalisar dinkin duniya, wajen magance matsalolin shaye-shaye, wanda suke ganin cewar ana kyale mata da wannan matsalar, ba’a basu kulawa ta musamman.

A ta bakin shugaban kungiyar Mr. Werner Sipp, kashi daya bisa uku, na mashaya a fadin duniya mata ne! Amma kaso daya bisa biyar ne, kawai suke samun kulawa ta musamman. Hakan na nuni da cewar ana nuna wariya a tsakanin mata da maza. Akan horas da mata fiye da irin horon da akanyi ma maza mashaya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG