Wani sabon bincike da taron masana suka gabatar, na bayyanar da yadda manhajojin da mutane kan saukar a wayoyinsu, na zama hanyoyi da ake amfani da su don satar bayanan mutun batare da sanin shi ba.
Masanan da suka fito daga jami’ar ‘Virginia Tech’ ta kasar Amurka, waddan da suka zama na farko a duniya da suka gabatar da bincike, akan yanda manhajojin waya ke zama hanyar satar bayanan mutun. A wani tsari da suke kira ‘Yi magana da wani don bashi damar daukar bayananka’.
Sun kara da cewar akwai hanyoyi guda biyu, na daya shine manhaja da idan mutun ya saukar da ita, ya bada damar satar bayanan shi, na biyu kuwa shine wasu manhajojin wadanda aka kirkira batare da sanin ko wadanda suka kirkiresu sun saka musu matakan kari ba.
Kamar misali manhajar da ke da fitila da mutane kanyi amfani dasu a wayoyi, da yawan su, sukan dauki bayanan sirri da lambobin, da inda mutun yake, don bada su ga makirkira manhajar 'Yan-kutse'.
Masanan sun gabatar da binciken ne a kan wasu manhajoji 100,000 a shafin Google Play, da sama da manhajoji 10,000 a shafin malware app. Sun kara da cewar akwai matukar bukatar mutane, su san wadannen irin manhajoji suke saukarwa a wayoyin su don gujema satar bayanai.