Wanda ya kirkiri shafin yanar gizo na Wikipedia ya fara wani sabon shafin na yanar gizo inda yace zai yi yaki da labarun da ake kira na karya.
Sabon shafin da Jimmy Wales ya kirkira mai suna Wikitribune zai yi aiki da yan jaridu da kuma masu budo gaskiya na sakai a waje guda domin yaki da labaran karya.
Shafin kungiyar yanar gizon ya bayyana cewar “Muna son mu tabbatar da kun karanta labaran da aka gina su da gaskiya, wadanda ke da amfani akan abubuwan dake faruwa a kanana da kuma fadin duniya,”
Aikin masu duba gaskiyar al’amuran masu zaman kansu yayi kama da yadda Editoci ke aiki a shafin Wikepedia. Ko wanne sauyi aka samu wasu masu duban gaskiyar al’amuran dabanne zasu duba.
Haka kuma shafin zai karbi labarai daga hannun kwararrun ‘Yan jarida. Sabon shafin na Wikitribune zai rika rattaba cikakkun labarai da kuma tattaunawa a rubuce sabanin sauran kafafen yada labarai.
Kafar yada labarai ta CNN ta bada rahoton Wales na cewa “Sun dauki kwararrun matakan aiyukan jarida tare da sababbin tunani masu juya hankali daga duniyar Wiki da al’ummar da ke aiyukan sakai domin kare martabar bayanan da aka samu,”
Haka kuma za’a tafiyar da wannan shafi ne ta hanyar karbar gudummawa sabanin tallace tallace ko kuma yin rijista da sauran shafuka ke yi.
Wales ya kara da cewa “ana gina labaran karyane domin a nuna wa mutane abinda suke son gani, domin tabbatar da son ransu da kuma sa su dukufa wajen duba shafukan a kowanne irin hali. Wanda ya sabawa Dalilin aikin jarida.