Daga tsarin daukar kudade a jiki, zuwa tsarin amfani da kati wajen biyan kaya ko aika kudi ta asusun banki, har zuwa tsarin biyan kudin mota da wayar hannu, ko siyan abinci. Duk wannan wani sabon tsari ne da duniya ta cigaba da shi.
Kasashen Afrika ba’a barsu a baya ba, domin kuwa ‘yan kasuwa masu karamin karfi na cin gajiyar wadannan hanyoyin na kimiyya da fasaha. Haka yanar gizo ta taimaka matuka wajen ganin jama’a sun samu karuwar wayewar kai.
Maria Sarungi, matashiya ce da ta kirkiri wani shafin yanar gizo a kasar Tanzania, wanda suke bincike da bibiyar yadda gwamnati ke gudanar da ayyukan su, da tankade da rai-raya wajen ganin an kawo adalci a cikin jama’a.
Tace ada yadda mutane ke zama a bakin hanya suna tattauna matsalar su, da bata zuwa ko ina, amma yanzu mutane kan shiga shafin don bayyanar da wani abu da akayi bisa rashin gaskiya, sukan bi kadin abun da kokarin kwatoma jama’a hakkin su.
A iya nata fahimtar, yanar gizo wata hanyace mai amfani ba kawai ga ‘yan boko ba, da yadda ake kallon abun, wannan wata hanyace da kowa zai bayyanar da abun da ke damun shi da kuma neman mafita.
Haka a kasar Uganda, wasu matasa sun kirkiri irin wannan shafin, wanda suke bayyanar da irin ra'ayoyin su dangane da abun dake faruwa a yankunan su. Mutane da dama suna cin gajiya wannan damar. Domin kuwa gwamnati tana bibiya da irin abubuwan da suke rubutuwa don kawo gyara a tsakani.
A kasar Kenya kuwa, irin tsarin yana da matukar tasiri, musamman wajen bincike da yadda ‘yan siyasa ke gudanar da ayyukan su, batare da handama da babakere na dukiyar jama’a ba.
Hakan wata damace da ya kamata ace matasa a koina suna amfani da shafufukan yanar gizo, wajen kara wayar da kan jama’a da basu damar bayyana ra’ayoyin su.
Facebook Forum