Anthony Joshua, matashi dan asalin Najeriya, kuma shahararren dan wasan damben Boxing na duniya, zai kara da fittaccen dan wasan damben boxing na kasar Bulgaria, Kubrat Pulev. Joshua, ya gagari kowa a fagen damben boxing, inda ya lashe kambu na zama matashi da yafi karfi a duniyar wasan damben boxing.
Kubrat, mai shekaru 36, ya tabbatar da cewar zai kara da matashi Joshua, badan yana soba, sai don ya nuna ma duniya cewar shine zakara, amma ya zuwa yanzu yana kara shiryawa don ganin yayi nasara akan matashin.
Ya kara da cewar, lallai matashin abun tsoro ne, domin kuwa yana da wasu dabaru da idan mutun bayi hankali ba, babu yadda mutun zaiyi da shi. Amma yanzu ya fahimci irin dabarun matashin, kuma zai kokarta wajen ganin ya kwace kambun daga hannun sa.
Kubrat ya cigaba da cewar, bazan ba matashin wata dama ba, muddun muka shiga fagen daga, zamu kara a birnin Cardiff, na kasar Birtaniya, a ranar 28 ga watan Oktoba, idan Allah ya kai rai. Tabbas matashin yana da hadari gaskiya, amma a shirye nake.
Har a dai-dai hada wannan labarin, bangaren matashi Joshua, basu amsa wannan gayyatar ba, ko zasu yarda su kara da tsohon dan wasan. Ana dai sa rai yau Talata su fitar da wata sanarwa.
Facebook Forum