Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kishi Kumallon Mata


Bilyaminu da Maryam
Bilyaminu da Maryam

Bilyaminu Muhammad Bello, dan tsohon shugaban jamiyyar PDP, Haliru Bello, ya gamu da ajalinsa a hannun matarsa ta aure Maryam Sanda, wacce ake zargin cewa ta kashe shi sanadiyar wata ‘yar rashin jituwa da ta rikide ta zama babba.

Rahotanin na nuni da cewa lamarin ya faru ne biyo bayan zargin da Maryam kewa mijinta na neman wata budurwa bayan da ta ga wani sakon karta kwana da aka aika masa dashi.

Gawar mamacin ta nuna cewar an sokeshi sau uku a bayansa da kuma sau da dama a mazakutarsa wannan lamari dai ya faru ne a gidansu dake unguwar Maitama a babban birni tarayyar Najeriya Abuja.

Bayan aikata wannan aika aika da ake zarginta da aikatawa sai ta kai shi asibiti inda daga bisani rai yayi halinsa suna da ‘ya daya mai suna Sa’adatu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG