Kocin tawagar kasar Ingila Gareth Southgate na shirin sanya hannu a sabuwar kwangilar shekaru hudu domin zama kocin Ingila a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a shekara ta 2022.
Kocin mai shekaru 48, da haihuwa wanda kwantiraginsa na yanzu zai ƙare a shekara ta 2020, ya jagoranci tawagar Ingila, zuwa gasar cin kofin duniya na bana, inda ya samu nasarar kai kasar wasan dab da na karshe a karon farko tun bayan shekaru 28, da suka wuce, Kocin ya amince da Karin wa'adin da zai karbi kudin har fan miliyan 3 a shekara.
Wani Rahoto daga Manchester united, ya ce duk da takun sakar da ake samu tsakanin 'yan wasanta da kocin ta Mourinho Shugaban kungiyar Ed Woodward ya goyi bayan Mourinho kuma ya ce baya tunanin sallamar mai shekaru 55 din.
Duk da haka, 'yan wasa da dama suna la'akari da barin kungiyar a karshen kakar wasa idan Mourinho, ya ci gaba da janragamar kulob din, aranar laraba an samu takun saka tsakanin Jose Mourinho, da dan wasan tsakiyar Manchester united, Paul Pgoba, a filin atisaye.
Mourinho, ya ajiye Pgoba, a wasan da kungiyar ta yi da Derby County, a kofin Caraboa, ranar Talata inda Derby ta yi waje da Manchester da ci 8-7 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan sun yi 2-2.
Tun kafin wannan sa-in-san Mourinho, ya karbi matsayin Pgoba, na mataimakin Kaftin a kungiyar.
Facebook Forum